Home gida ALMUNDAHANA: Kotu Ta Kara Kwace Gidajen Diezani

ALMUNDAHANA: Kotu Ta Kara Kwace Gidajen Diezani

431
0
SHARE

Wata babbar kotun tarayya da ke Legas, ta bada umurnin a sake kwace wasu manyan gidajen alfarma na tsohuwar ministar mai Diezani Alison Madueke.

Kotun ta ce ta kwace gidajen ne a  rukunin gidajen na tsibirin Banana, da kuma rukunin gidaje na Admiralty da ke karamar hukumar Ikoyi a jihar Legas.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta ce kimar kudaden gidajen a kasuwa za ta kai dala miliyan 4.76.

Idan dai ba a manta ba, kwanakin  baya Kotun ta sake bada umurnin kwace wasu gidajen na tsohuwar ministar da yawan su ya kai 58.

LEAVE A COMMENT