Home gida ALMUNDAHANA: Kotu Ta Wanke Sanata Yeriman Bakura

ALMUNDAHANA: Kotu Ta Wanke Sanata Yeriman Bakura

414
0
SHARE

Wata babbar Kotu a jihar Zamfara ta sallami karar da hukumar ICPC ta shiga bisa zargin tsohon gwamnan jihar Zamfara Ahmed Sai Yeriman Bakura.

Idan dai za a iya tunawa, tun a watan Janairu na shekara ta 2016 ne ICPC ta maka Sanata Yarima kotu, bisa zargin sa da kakartar da naira biliyan daya da aka ware da nufin gyaran madatsar ruwa ta Gusau, inda ta ce kudin an samo su ne daga bashin Banki.

Bello Muhammad Tukur dai ya yi watsi da dukkan tuhume- tuhume 19 da ICPC ke yi wa Sanata Yarima, bayan lauyan wanda ake kara ya ce Yarima bai taba yi wa kan sa, ko abokai ko ‘yan’uwan sa alfarma ba a zamanin mulkin sa.

Da ya ke zantawa da manema labarai, Sanata Ahmad Sani ya yaba da hukuncin Kotun, inda ya ce gaskiya ta yi halin ta, domin a cewar sa, tun farko ya san  bai aikata ba daidai ba.

LEAVE A COMMENT