Home gida ALMUNDAHANA: Kudaden da Muka Gano a Hannun Diezani Somin Tabi Ne –...

ALMUNDAHANA: Kudaden da Muka Gano a Hannun Diezani Somin Tabi Ne – EFCC

501
0
SHARE

Shugaban hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Ibrahim Magu ya ce kudaden da hukumar ta samu daga hannun tsohuwar ministar man fetur, Diezani Allison Madukwe bai kai cikin cokali ba daga cikin kudaden da tayi sama da fadi dasu.

Magu ya ce bayan tsananta bincike kan zargin da ake yiwa ministar, EFCC ta gano tsabar kudaden sama da naira biliyan 47 da wasu Dala miliyan dari 4 da 87 da wasu gidaje da kadarori a hannun ta.

Shugaban hukumar ya ce suna ci gaba da aiki da wasu hukumomin kasashen duniya domin gano wasu tarin dukiyar da tsohuwar ministar ta mallaka.

Tuni dai kasashen Amurka da Birtaniya suka kaddamar da bincike kan ministar saboda zargin halarta kudaden haramun.

Haka zalika Magu ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba, a kokarin yaki da cin hanci da rshawa duk da barazana da yake fuskanta daga bangarori da dama.

LEAVE A COMMENT