Home gida BIKIN ‘YAR GANDUJE: Shiekh Gumi Ya Ce An Yi Barnar Dukiya Ne

BIKIN ‘YAR GANDUJE: Shiekh Gumi Ya Ce An Yi Barnar Dukiya Ne

898
0
SHARE
Dr. Ahmad Abubakar Gumi

Sheikh Ahmad Mahmud Abubakar Gumi ya yi Allah-Wadai da barnar dukiyar da aka yi a wajen daurin auren ‘yar gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da dan gwamna Ajimobi na jihar Oyo.

 

Shehin ya ce duk da N50, 000 ne kudin sadakin auren, an yi wahala an kuma barnatar da dimbin dukiyar da shugabanni za su iya yi wa Talakawa aiki da su.

 

Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata ‘yar Fatima Ganduje ta auri dan Gwamnan Jihar Oyo Idris Abiola Ajimobi, inda manyan Nijeriya daga ko ina su ka cika garin Kano domin halartar daurin auren.

 

Sheikh Gumi, ya ce addinin Musulunci bai yarda da barna da dukiyar al’umma ba, inda ya ce abin da ake bukata wajen daurin aure kurum shi ne tsirarrun shaidu, amma ba Shugabanni su kona man jirgi ba domin zuwa biki.

 

Malamin, ya kuma yi tir da yadda ma’auratan su ka rika daukar hotunan da ba su dace ba ana yadawa.

LEAVE A COMMENT