Home gida BINCIKE: Ba Zan Amsa aTambayoyin Majalisar Dattaw Ba – IG

BINCIKE: Ba Zan Amsa aTambayoyin Majalisar Dattaw Ba – IG

301
0
SHARE

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Ibrahim Idris, ya ce ba zai amsa tambayoyin da kwamitin majalisar dattawa ya yi masa ba domin maganar ta na kotu.

 

Ibrahim Idris, ya ce yin hakan saba wa dokar kasa ne da kuma dokar majalisar dattawa.

 

Majalisar dai ta bukaci ya bayyana a gaban ta domin yi mata bayani a kan wasu zarge-zarge da ake yi masa da Sanata Isah Misau ya zayyana a zauren majalisar.

 

Sai dai shugaban kwamitin Francis Alimikhena, ya ce kotu ce ta ke neman ta tsoma bakin ta a cikin aikin su, domin majalisar ta kafa wannan kwamitin kafin a kai maganar gaban kotu, ya na mai cewa abin da su ke yin bincike a kai daban da wanda ke gaban kotu.

 

Kwamitin ya ce zai buba bayanan da aka gabatar ma shi, zai kuma sake gaiyatar Ibrahim Idris ya domin ya bayyana a gaban sa.

LEAVE A COMMENT