Home gida BOKO HARAM: Hankula Sun Kwanta A Garin Gulak Na Jihar Adamawa

BOKO HARAM: Hankula Sun Kwanta A Garin Gulak Na Jihar Adamawa

203
0
SHARE

Daruruwan mazauna garin Gulak da ke karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa sun koma gidajen su, bayan jami’an sojin Nijeriya sun samu nasarar dakile kazamin harin da mayakan Boko Haram su ka yi yunkurin kaddamarwa.

 

A ranar litinin da ta gabata ne, ‘yan Boko Haram su ka yi kokarin kutsawa cikin garin Gulak, inda sojoji su ka tare su aka kuma cigaba da fafatawa tsawon sa’o’I, kafin daga bisani sojojin su yi nasarar fatattakar su.

 

Har yanzu dai babu cikakke bayani a hukumance kan yawan wadanda su ka rasa rayukan su, sai dai wata majiya ta ce sojoji uku sun rasa rayukan su, yayin da aka kashe wani adadi mai yawa daga bangaren mayakan Boko Haram.

 

Harin dai ya zo ne bayan wasu maza biyu ‘yan kunar bakin wake sun tarwatsa kan su a wani gida da ke wajen garin na Gulak su ka hallaka wasu mutane biyu.

LEAVE A COMMENT