Home gida CI-GABAN KASA: Majalisar Zartarwa  Ta Amince Da Ciyo Bashin Dala Biliyan 2...

CI-GABAN KASA: Majalisar Zartarwa  Ta Amince Da Ciyo Bashin Dala Biliyan 2 Daga Ketare

238
0
SHARE

Majalisar zartarwa ta amince da ranto fiye da dala biliyan 2  daga kasashen waje domin gyare-gyare a zaman da ta yi na ranar Larabar da ta gabata.

Ministar kudi Kemi Adeosu ta bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala zaman majalisar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Adeosu ta ce za a yi amfani da Naira biliyan 762 wajen farfado da arzikin kasa.

Wasu rahotannin sun ce shugaban kasa Buhari ya canja sallon yadda ake gudanar addu’a a taron zauran majalisa, inda Buhari ya umurci Ministoci biyu mabiyya addinin Kirista Audu Ogbeh da Chris Nigige su bude taron da addu’a.

Bayan Ogbeh ya kammala addu’a sai Buhari ya umurci Ngige ya yi addu’a, sakamakon karamin Ministan Muhalli Jibrin Aminu bai halarci zaman majalisar ba.

Daukar wannan salo ya bawa Ngige mamaki inda ya tunatar da Shugaba Buhari cewa, shi Kirista ne amma Buhari ya umurce shi ya yi addu’ar.

LEAVE A COMMENT