Home gida CI-RANI: ‘Yan Nijeriya 2,778 Ke Tsare A Kasar Libya – Hukuma

CI-RANI: ‘Yan Nijeriya 2,778 Ke Tsare A Kasar Libya – Hukuma

180
0
SHARE
epa04428211 Migrants from sub-Saharan Africa rest after being rescued by the Libyan coastguard when their boat sank three natutical miles off the Libyan coastal town of Guarabouli, 60km east of Tripoli, Libya, 02 October 2014. According to media reports the Libyan coast guard has recovered at least ten dead bodies from the water, and rescued between 80-90 people though according to the survivors there may have been as many as 180 passengers onboard when the boat sank. EPA/STR

Gwamnatin Tarayya ta ce ta na da adadin ’yan Nijeriya har 2,778 da ke tsare a sansanoni daban-daban a kasar Libya, wadanda ake ta kokarin dawo da su Nijeirya.

A cikin wata sanarwa da jamai’in yada labarai na ma’aikatar Harkokin ketare Elias Fatile ya sanya wa hannu, ya ce jami’an ofishin jakadancin Nijeriya da ke Libya su na bin sansanoni da dama domin tantance yawan ’yan Nijeriya da ke tsare.

Ma’aikatar ta ce, duk wadanda aka kidaya sunan su, an yi ta ba su takardar iznin tafiya ko shiga Nijeriya ta gaugawa.

Sanarwar ta kara da cewa, hukumar ta na aikin hadin kai da kungiyar kula da masu gudun hijira, inda a kowane mako ana dauko ‘yan Nijeriya 250 daga Libya ana dawowa da su Nijeriyagida.

 Ya zuwa yau dai, ma’aikatar ta ce an dawo da ’yan Nijeriya 3000 gida.

LEAVE A COMMENT