Home gida CIN AMANA: AN TSARE SHUGABAN PDP NA JIHAR JIGAWA A GIDAN YARI

CIN AMANA: AN TSARE SHUGABAN PDP NA JIHAR JIGAWA A GIDAN YARI

446
0
SHARE

Kotun Majistare ta biyu da ke zama a birnin dutse na jihar Jigawa, ta tasa keyar shugaban jamiyyar PDP na jihar Alhaji Salisu Mahmuda da wasu tsofaffin mukarraban gwamnatin jihar zuwa gidan yari har zuwa ranar 23 ga wata Mayu domin yanke hukunci a kan bukatar bada belin su kamar yadda lawyoyi su ka bukata.

Ana dai zargin Alhaji Salisu Mahmud tare da tsofaffin kwamishinoni 5 da jami’an kungiyar shugabannin ma’aikatan kananan hukumomi ta ALGON da aikata laifuffuka 4, amma sun musanta.

Wadanda lamarin y shafa dai sun hada da shugaban jamiyyar PDP na jihar da wani Salisu Saleh Indirawa, da Nasiru Umar Roni, da Shehu Umar Chamo, da tsofaffin shugabannin kananan hukumomin Gagarawa Mukhtar Ibrahim Gongal, da na Kirikasamma Abba Mohammed Daguro.

Ana dai zargin mutanen ne da laifin cin amanar gwamnati, wanda hakan ya saba wa sashe na 97 da 312 da 123 da Kuma na 287 na dokar Final Code.

Yanzu haka dai alkalin kotun mai shari’a Usman Muhammed Lamin, ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Mayu na shekara ta 2017.

LEAVE A COMMENT