Home ENGLISH DIFILOMASIYYA: Buhari Zai Halarci Taron Kungiyar EU Da AU A Abidjan

DIFILOMASIYYA: Buhari Zai Halarci Taron Kungiyar EU Da AU A Abidjan

224
0
SHARE

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron kungiyar tarayyar Turai da na Afrika karo na 5 a birnin Abidjan na kasar Kodebuwa.

 

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Femi Adesina ya bayyana kaha a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce taron zai gudana ne daga ranar 28 ga watan Nuwamba zuwa 29.

 

Ya ce shugaba Buhari zai halarci taron, kuma zai gana da wasu shugabannin kasashen Afrika da na kungiyar tarayyar Turai.

 

Shugaba Buhari, zai yi amfani da wannan taron domin sake fadada shirye-shiryen Nijeriya na aiki tare da kasashen Afirka da Turai don magance matsalolin da su ka shafi zaman lafiya da tsaro.

 

Wata majiya ta ce shugabannin kasashen Afrika 55 da na tarayyar Turai 28 ne za su halarci taro mai girman.

 

Adesina, ya ce gwamnonin jihohin Akwa Ibom da Bauchi da wasu ministoci za su kasance daga cikin manyan jami’an gwamnatin da za su mara wa shugaba Buhari baya.

LEAVE A COMMENT