Home gida DOKAR ZABE: Sake Tsarin Ta Zai Amfani Masu Jefa Kuri’a – Ekweremadu

DOKAR ZABE: Sake Tsarin Ta Zai Amfani Masu Jefa Kuri’a – Ekweremadu

173
0
SHARE

Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ike Ekweremadu, ya ce majalisar dokoki ta kasa na son a sake tsarin dokar zabe ne saboda ta ba masu zabe damar tantance dan takara da kan su.

 

Ekweremadu, ya ce sake tsarin dokar zabe da majalisar wakilai ta gabatar, zai taimaka matuka domin zai ba masu zabe damar yanke hukunci a kan ‘yan takarar da ke neman kuri’un su a kowane.

 

Sanatan ya bayyana haka ne, a lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga hukumar kasashen Turai a Nijeriya karkashin jagorancin Mista Paul Akwright.

 

Idan dai za a iya tunawa, a baya dan majalisar Majalisar Wakilai Alhassan Ado Doguwa, ya ce sake tsarin dokar zabe da Majalisar ta yi ba komai ba ne ila zagon-kasa ga jam’iyyar APC da Shugaba Muhammadu Buhari.

LEAVE A COMMENT