Home gida HANA SHAYE-SHAYE: Sanata Ben Murray Ya Kalubalanci Sanatoci

HANA SHAYE-SHAYE: Sanata Ben Murray Ya Kalubalanci Sanatoci

525
0
SHARE

‘Yan majalisar dattawa sun ce dole a yi bincike game da yadda shan kayen maye ya zama ruwan dare a fadin Nijeriya.

 

Sai dai Sanata Sanata Ben Murray-Bruce daga Jihar Bayelsa, ya ce kamata ya yi Sanatocin su fara wannan binciken daga gidajen su.

 

Sanatan ya ce, mafi yawa daga cikin yaran da ‘yan majalisar su ka haifa su na cikin masu shan kayan mayen.

 

A cewar sa, matasa da dama ba su da aikin yi sai yawan shaye-shaye, inda ya ce abin da ya ke sa su zama cikin farin ciki kawai kenan.

 

Idan dai ba a manta ba, wani bincike ya nuna cewa daga Jihar Kano zuwa Jihar Jigawa ana shan akalla kwalabe miliyan 3 na Codeine a kowace rana.

LEAVE A COMMENT