Home gida IFTILA’I: Gobara Ta Tashi A Ofishin DPR Da Ke Minna A Jihar...

IFTILA’I: Gobara Ta Tashi A Ofishin DPR Da Ke Minna A Jihar Neja

123
0
SHARE

A Talatar da ta gabata ne,  wata gobara ta lashe ofishin Hukumar Kula da albarkatun man futer DPR da ke Minna a jihar Neja.

 

Rahottani sun ce gobarar da ta fara ci tun daga yammacin ranar Litinin, ta afku ne sakamakon tangardar wutar lantarki.

 

Yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a garin Minna, Shugaban sashen ayyukan na hukumar Injiniya Abdullahi Isah Jankara, ya ce gobarar ta fara ne daga dakin ayyukan intanet daga bisani ta bazu zuwa wasu ofisoshi guda hudu.

 

Ya ce ma’aikatan hukumar kashe gobara ta jihar ne su ka agaza wajen kashe gobarar.

 

Ofisoshin da su ka kone kuwa sun hada da Ofishin Akanta, da Ofishin shugaban sashen iskar gas, da ofishin shugaban tace danyen mai da kuma dakin samar da intanet.

LEAVE A COMMENT