Home gida INSHORAR LAFIYA: Shugaba Buhari Ya Maida Usman Yusuf Bakin Aikin Sa

INSHORAR LAFIYA: Shugaba Buhari Ya Maida Usman Yusuf Bakin Aikin Sa

156
0
SHARE

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya maida shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa Usman Yusuf bakin aikin sa.

 

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya tabbatar wa manema labarai haka.

 

Idan dai ba a manta ba, da yammacin ranar Alhamis da ta gabata ne, ministan lafiya Isaac Adewole ya dakatar da shugaban hukumar inshorar lafiya ta Kasa Usman Yusuf daga aiki.

 

An dai tuhumi Usman Yusuf ne da yin amfani da wasu kudade kimanin naira Miliyan 200 domin horar da wasu ma’aikatan hukumar da kuma rashin jituwa da ke tsakanin sa da ministan.

 

Isaac Adewole, ya ce wasu daga cikin dalilan da su ka sa ya dakatar da shugaban hukumar shi ne, domin korafe-korafen da ake ta yi akan sa na sama da fadi da wasu kudaden ma’aikatan da kuma zargin shi da aikata wasu laifuffukan da su ka saba wa dokar ma’aikatar.

 

Rahotanni sun ce tuni shugaba Buhari ya umurci Yusuf Usman ya koma aikin sa, su kuma daidaita kan su domin ci-gaban ayyukan ma’aikatar.

LEAVE A COMMENT