Home HAUSA JAGORANCI: Farfesa Ango Abdullahi Ya Zama Shugaban Dattawan Arewa

JAGORANCI: Farfesa Ango Abdullahi Ya Zama Shugaban Dattawan Arewa

404
0
SHARE

Kungiyar Dattawan Arewa ta nada Farfesa Ango Abdullahi a matsayin sabon Shugaban ta, kuma shugaban kwamitin amintattu.

 Shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar Mohammed Bello Kirfi, ya ce sun yi wani taro na musamman a ranar Larabar da ta gabata a Abuja, inda su ka dauki mataki game da kungiyar da kuma halin da Nijeriya ke ciki.

 Kirfi ya cigaba da cewa, bayan taron ne su ka shirya nadin wasu kwararru da za su jagoranci ragamar Kungiyar ta Arewa.

 Sauran wadanda aka nada su jagoranci kungiyar kuwa sun hada da Alhaji Sani Zangon-Daura a matsayin Mataimakin shugaba.

 Sauran sun hada da Yahaya Kwande da Janar Paul Tarfa, da Sam Nda Isiah, da Hakeem Baba-Ahmed da sauran su.

LEAVE A COMMENT