Home gida KIRANYE: KOTU Za ta Yi Zama Kan Melaye Ranar 11 Ga Watan...

KIRANYE: KOTU Za ta Yi Zama Kan Melaye Ranar 11 Ga Watan Satumba

303
0
SHARE

Babbar kotun tarayya dake Abuja, ta sanar da ranar ranar 11 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta yi zama kan batun kiranye da ‘yan mazabar Kogi ta yamma ke kokarin yiwa dan majalisarsu Dino Melaye.

Mai shari’a Nnamdi Dimgba, na kotun ya sanar da haka a bayan ya saurari lauyoyin bangarorin biyu inda suka tafka muhawara akan batun.

Wannan na zuwa ne bayan Melaye, ya shigar da kara inda ya kalubalanci sanya hannun wasu daga cikin mutanen da suka sanya hannun amincewa da kiranyen.

Al’ummomin yankin dai sun yanke hukuncin yiwa dan majalisar kiranye ne bayan sun yi zargin cewa bai musu wakilci na gari a majalisar dattawa.

LEAVE A COMMENT