Home gida KIWON LAFIYA: A’ISHA BUHARI TA KADDAMAR DA GININ ASIBITI A DAURA

KIWON LAFIYA: A’ISHA BUHARI TA KADDAMAR DA GININ ASIBITI A DAURA

773
0
SHARE

Uwargidar shugaban kasa A’isha Muhammadu Buhari, ta kaddamar da ginin wani asibiti mai cin gadajen jinya 50 a garin Daura da ke jihar Katsina domin kula da lafiyar mata da kananan yara.

Da ta ke jawabi a lokacin kaddamar da ginin, Aisha Buhari ta ce za ta gina asibitin ne domin agaza wa marasa galihu da miskinai a fadin Nijeriya.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, za a gina asibitin ne a karkashin shirin uwargidar shugaban kasa mai taken ‘Future Assured’ a Turance, a matsayin wani bangare na taimako domin rage mace-macen masu juna biyu da kananan yara a fadin Nijeriya.

A’ish Buhari dai, ta yi alkawarin gina irin wannan asibiti a dukkan sauran yankuna 6 da ke fadin Nijeriya.

LEAVE A COMMENT