Home gida KORAFI: ‘YAN BOKO HARAM SUN DAWO DAJIN TARABA- DARIUS

KORAFI: ‘YAN BOKO HARAM SUN DAWO DAJIN TARABA- DARIUS

499
0
SHARE

Gwamnan jahar Taraba Darius Ishaku ya koka a kan yadda mayakan Boko Haram da aka koro daga dajin Sambisa ke samun mafaka a dajin Suntai da ke jihar.

Darius ya bayyana wa kwamandan runduna ta 82 Manjo Janar Adamu Abubakar haka ne a Enugu, yayin da ya kai masa ziyara ranar Alhamis da ta gabata a Jalingo.

Ya ce tun farko da aka fara samun kwararar mutane cikin jihar, ya koka a kan yiwuwar wannan matsala, amma sai aka zarge shi da yunkurin kin jinin baki.

Ya ce yanzu haka mutane ba su iya tafiya akan hanyar Bali zuwa Suntai da Takum ba tare da su na cikin fargaba ba.

LEAVE A COMMENT