Home gida KORAFI: Za a Yi Wa Rundunar ‘Yan Sandan SARS Garambawul

KORAFI: Za a Yi Wa Rundunar ‘Yan Sandan SARS Garambawul

122
0
SHARE

Sufeta Janar na ‘yan Sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya bayar da umarnin sake fasalin rundunar ‘yan sanda ta musamman da ke yaki da ‘yan fashi da makami watau SARS.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da ‘yan Najeriya suka yi ta suka a shafukan sada zumunta game da zargin rundunan ‘yan sandan na SARS da cin zarafin al’umma.

Masu rajin kare hakkin dan Adam da sauran masu ruwa da tsaki a lamarin sun yi ta amfani da maudu’in na End SARs a shafin sada zumunta na Twitter, domin kiran a kawo karshen rundunar.

Wani mai amfani da shafin sa da zumunta na Twitter mai adireshen @YabaKid, ya yi ikirarin cewa a gabansa wasu jami’an SARs suka harbi wani yaro a kai.

Rundunar ‘yan sanda dai ta fitar da lambobin wayoyi da adireshin email da wasu kafofin sada zumunta, inda ta bukaci mutane su kai koken su na cin zarafin da suke zargin an yi musu, don a bincika tare da daukar matakan da suka dace.

LEAVE A COMMENT