Home HAUSA KUDIN MAKAMAI: EFCC Ta Kara Gurfanar Da Anyim Pium Anyim

KUDIN MAKAMAI: EFCC Ta Kara Gurfanar Da Anyim Pium Anyim

201
0
SHARE

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Anyim Pius Anyim ya shiga tsaka mai wuya, bayan hukumar EFCC ta bankado yadda ya karbi naira miliyan 575 a matsayin kudin ayyukan musamman daga ofishin Kanar Sambo Dasuki. 

Jami’an hukumar EFCC dai su na binciken gano irin ayyukan musamman da Anyim ya gudanar da kudin, alhalin ba shi ne ministan ayyuka na gwamnatin tarayya ba.

Binciken hukumar EFCC ya tabbatar da cewa, Anyim ya saka hannun karbar kudi Naira miliyan 500 a ranar 4 ga watan Maris na shekara ta 2015 daga ofishin Kanar ASambo Dasuki. 

Haka kuma, EFCC ta kara samun wasu bayanai da ke nuna Anyim ya kara karbar Naira miliyan 20 a ranar 14 ga watan Maris na shekara ta 2015 daga ofishin Kanar Sambo Dasuki, bayan ya taba karbar naira miliyan 30 a ranar 24 ga watan Mayu na shekara ta 2013.

LEAVE A COMMENT