Home gida KWANGILOLI: Buhari Ya Amince A Fifita ‘Yan Nigeria Akan ‘Yan Kasar Waje

KWANGILOLI: Buhari Ya Amince A Fifita ‘Yan Nigeria Akan ‘Yan Kasar Waje

147
0
SHARE

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince a rika ba ‘yan Nijeriya fifiko a kan ‘yan kasashen waje wajen bada kwangiloli.

 

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke sanya hannu a kan wasu takardun dokar shugaban kasa a fadar sa da ke Abuja.

 

A cikin dokar, Shugaba Buhari ya ba hukumomi da ma’aikatun gwamnati umarnin su rika bada kamfanonin cikin gida fifiko wajen tsarawa da aiwatar da ayyukan tsaron kasa.

 

Shugaba Buhari, ya ce ya dauki matakin ne domin kara samar da ayyuka ga ‘yan Nijeriya.

 

Sai dai ya ce za a ba kamfanonin waje dama idan har na cikin gida ba su da kwararrun da za su aiwatar da wani aiki da kwangilolin da gwamnati ke son su yi.

 

Shugaba Buhari, ya kuma haramta wa ma’aikatar cikin gida bada yan kasashen wajen da za su shigo Nijeriya biza domin gudanar da duk ayyukan da akwai wadanda za su iya yin su a Nijeriya. 

LEAVE A COMMENT