Home gida MARTANI: Farfesa Jega Ya Ce Kayyade Yawan Jam’iyyu A Nijeriya Ba Dai-Dai...

MARTANI: Farfesa Jega Ya Ce Kayyade Yawan Jam’iyyu A Nijeriya Ba Dai-Dai Ba Ne

193
0
SHARE

Tsohon shugaban hukumar zaben ta kasa INEC Farfesa Attahiru Jega ya ce bai kamata ace an kayyade yawan jam’iyyun siyasar Nijeriya ba, saboda dimokradiyya a ko ina a kan bari duk wanda yaga zai iya kafa jam’iyya, sai ya fito ya kafa, sannan kuma ya yi kokarin jan ra’ayi jama’a wadan da za su mara masa baya har su samu nasara idan lokaci zabe ya yi.

Jega ya bayyana hakane ga manema labarai a matsayin ra’ayin sa kan shawarar da tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayar a kan takaita yawan jam’iyyun siyasa zuwa biyu kadai.

Ya ce kasashe da suka ci gaba, babu wadda aka  bukaci tantance yawan jam’iyyun su, domin yawan jam’iyyu da suka fito zai bada damar  tantancewa wasu har su yi karfi.

Jega ya ce a ba mutane zabi a hankali sai su fahimci waccece jam’iyyar gaskiya da zasu karkata a kanta.

A karshe ya ce lokacin da ya rage a gudanar da zabe a Nijeriya ba zai ba wata jam’iyya dama da zata fito damar samun  kafuwa ba, sai dai idan wasu jam’iyyun ne za su hadu domin yin hadaka, suma akwai  kokanto lokaci ya kure masu.

LEAVE A COMMENT