Home HAUSA RAJISTAR ZABE: Kamfanin Facebook Ya Ce Zai Taimaka Wa INEC

RAJISTAR ZABE: Kamfanin Facebook Ya Ce Zai Taimaka Wa INEC

118
0
SHARE

Dandalin sada zumunta na Facebook, ya ce a shirye ya ke ya taimaka wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta Kasa INEC, wajen wayar da kan ‘yan Nijeriya su yi rajistar zaben shekara ta 2019.

Hukumar zaben ta ce, furucin ya fito ne daga bakin wata tawagar musamman daga kamfanin Facebook a karkashin jagorancin Daraktan Yada Labarai na Afrika Ebele Okobi, yayin da su ka kai wa Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ziyara a ofishin sa da ke Abuja.

Misis Okobi ta ce, sun yi nazarin cewa daga cikin masu amfani da shafin Facebook a Nijeriya, mafi yawa sun fi tattauna batun da ya shafi zaben shekara ta 2019 ne da kuma siyasa.

Ta ce jama’a su na sa ido, kuma sun damu matuka dangane da yadda ake mulkin su, wadanda ke shugabantar su da kuma irin tafiyar gwanati.

A karshe ta ce kamfanin su ya bar kofa a bude, domin ganin sun bada gagarumar gudummawa wajen inganta harkokin zabe a yankin Afrika, musammamn ma Nijeriya.

 

LEAVE A COMMENT