Home HAUSA RIKICI SYRIA: Dakarun Gwamnati Na Cigaba Da Kai Hare-Hare Akan ‘Yan Tawaye

RIKICI SYRIA: Dakarun Gwamnati Na Cigaba Da Kai Hare-Hare Akan ‘Yan Tawaye

208
0
SHARE

Dakarun gwamnatin Syria da na Rasha na zafafa kai hare-haren sama a yankin da ke karkashin ikon ‘yan tawaye tun bayan da aka harbo wani jirgin yakin Rasha a karshen makon da ya gabata.

An kuma samun rahotannin harin gubar Iskar gas, sai dai  Gwamnatin Syria ta sha yin watsi da zargin da ake mata cewa tana kai hari da makamai masu guba.

Harin baya-bayan nan dai, shine na yankin Idlib da har yanzu ke karkashin ikon ‘yan tawaye, sai dai wasu rahotanni sun ce an samu wasu hare-haren a birnin Damascus a cikin wannan shekarar.

LEAVE A COMMENT