Home gida RIKICIN ZARIA: ‘Yan Shi’a Sun Nemi A Biyu Su Diyyar Miliyoyin Naira

RIKICIN ZARIA: ‘Yan Shi’a Sun Nemi A Biyu Su Diyyar Miliyoyin Naira

373
0
SHARE

Kungiyar mabiya akidar Shi’a sun shigar da karar Gwaman Jihar Kaduna, da Mallam Nasiru El-Rufa’i a wata kotun tarayya da ke zama a Kaduna, bisa tuhumar sa da cin zarafin su da kuma keta haddin su.

Masu shigar da karar da su ka hada da Injiniya Yahaya Gilima Karofi, da Muktar Abdullahi Muhammed da Aliyu Umar sun bayyana cewa, a na hana su gudanar da ibadar su, wanda hakan sun ce ya saba wa kundin tsarin mulki da kuma hakkokin bil adama.

Daga cikin wadanda aka shigar da karar a kan su kuma akwai Kwamishinonin ‘yan Sanda da na Shari’a da kuma Daraktan hukumar tsaro ta DSS na Jihar Kaduna, da Alkalin Alkalai na Gwamnatin Tarayya, da Sifeta Janar na ‘yan Sanda, da kuma Shugaban Rundunar Sojin Kasa.

‘Yan shi’ar dai su na neman a biya su diyyar naira miliyan dubu 100 tare da fitowa karara a idon duniya a nemi afuwar su, tare da bukatar kotu ta janye haramta al’amurran su da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi.

LEAVE A COMMENT