Home gida SABA DOKOKI: Kamfanin NNPC Ya Kama  Manajoji Biyu Da Laifin Karkatar Da...

SABA DOKOKI: Kamfanin NNPC Ya Kama  Manajoji Biyu Da Laifin Karkatar Da Lita Dubu 66

261
0
SHARE

Kamfanin matatan mai fetur na kasa NNPC ya ce ya tsananta kama ‘yan kasuwan man fetur masu laifi da yan bunburutu domin hukunta su.

Mai magana da yawun kamfanin Mista Ndu Ughamadu ya bayyana hakan a Abuja, ya ce sun kudiri yin haka ne domin tsabtace harkar siyar da man fetur da kuma kawar da dogayan layuka da a ke samu a gidajen mai.

Ya ce an kama ‘yan bunburutu 6 da manajojin gidajen mai biyu da laifin karkatar da lita dubu 66, kuma za a ci su tarar kowacce lita guda akan Naira 250.

Kamfanin dillancin labarai NAN ya ce ‘yan bunburutun kuma Alkali ya yanke masu hukunci zama a gidan yari na tsawan watanni 2 ko su biya tarar naira dubu 2, kuma nan take suka buya kudaden tarar.

LEAVE A COMMENT