Home gida SAMAR DA AYYUKANYI: Za a Shigo da Itatuwa Daga Kasar Malesiya

SAMAR DA AYYUKANYI: Za a Shigo da Itatuwa Daga Kasar Malesiya

355
0
SHARE

Hukumar kulda da harkokin daukar ma’aikata ta Najeriya ta ce za ta shigo da wasu itatuwan masu kayayyakin amfani tare da daukar matasa kimanin dubu 5 aikin kula da tatuwan.

Shugaban hukumar Nasiru Ladan, ya sanar da haka a lokacin da yake magana da ‘yan jaridu a babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce za a shigo da itatuwan ne wadanda suke girma a cikin watanni 12 daga kasar Maleysia, inda matasan da za a dauka za su rika kula da sun a tsawon wannan lokaci.

Ladan, ya ce an tattauna da gwamnatocin jihohi da kuma masu ruwa da tsaki domin samar da fili da za a dasa wadannan itatuwa da za a shigo dasu.

Ya ce hukumar za ta kuma maida hankali wajen horas da mutanen da za su rika kula da itatuwan domin ganin shirin ya kai ga nasara.

LEAVE A COMMENT