Home gida SAMAR DA LANTARKI: Fashola Ya Ce Shugaba Buhari Ya Damu Matuka Aakan...

SAMAR DA LANTARKI: Fashola Ya Ce Shugaba Buhari Ya Damu Matuka Aakan Matsalar

373
0
SHARE

Ministan wutar Lantarki da gidaje Babatunde  Raji Fashola ya ce samar da wutar lantarki ga al’ummar Nijeriya shi ne babban burin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Fashola ya kara da cewa, tunn daga shekarar 2015 da shugaban kasa Buhari ya kama ragamar gwamnnatin Nijeriya sun yi rawar gani matuka.

Ya ce kamfanin wutar lantarki na Azura mallakar ‘yan kasuwa da ke jihar Edo  yana  samar da Megawatt 450 daga cikin Megawatt fiye da dubu 7 da ake amfani da shi a fadin kasar’nan.

Fashola ya ce gwamnatin APC ta kashe dala biliyan biyu wanda ya lunka abin da gwamnatin PDP ta samar a shekara 16 na abunda ta ce ta kashe dala biliyan 20, a kasha kuma ta siyar da kamfanin NEPA ga ‘yan kasuwa da abokan ta.

Matsalar wutar lantarki a Nijeriya dai, ta zama ruwan dare sakamakon yawan dauke ta ake yi a koda yaushe da kuma tsufan kayan aiki da rashin biyan kudin wutar da dai sauran su.

LEAVE A COMMENT