Home gida SANARWAR BOGI: ‘Yan Sanda Na Neman Mai Magana Da Yawun IBB

SANARWAR BOGI: ‘Yan Sanda Na Neman Mai Magana Da Yawun IBB

123
0
SHARE

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta baza komar neman mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida wato Kassim Afegbua.

 

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Jimoh Moshood ya fitar, ta ce shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya bada umarnin a kama Mista Afegbua, sakamakon fitar da sanarwar bogi da bata suna, lamarin da zai iya janyo rigima a Nijeriya.

 

A karshen makon da ya gabata ne, Mista Afegbua ya fitar da sanarwar da ke cewa Janar Babangida ya ce kada a zabi Shugaba Buhari a zaben shekara ta 2019.

 

Sai dai Janar Ibrahim Babangida ya karyata sanarwar, inda ya ke musanta cewa rahotannin ba su yi daidai da kalaman da ya yi amfani da su ba a cikin sanarwar sa.

LEAVE A COMMENT