Home gida SAUYA FASALIN NIJERIYA: Yankin Arewa a Shirye Ya Ke – Ango Abdullahi

SAUYA FASALIN NIJERIYA: Yankin Arewa a Shirye Ya Ke – Ango Abdullahi

473
0
SHARE

Tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria Farfesa Ango Abdullahi, ya ce yankin arewa a shirye ya ke ko da Nijeriya za ta rabe.

 

Ango Abdullahi, ya ce arewa a shirye ta ke ta koma kan tsarin shekara ta 1914 kafin a kirkiri gamammiyar Nijeriya.

 

Farfesan ya bayyana haka ne, a wani taron kwana biyu da aka gudanar a kan nazarin bunkasa yankin arewa da ya gudana a Kaduna.

 

Ya ce Arewa ba ta tsoron komawa kamar yadda a ke kafin a hade Nijeriya a matsayin kasa guda.

 

Farfesa Ango ya kara da cewa, matukar ana so a sauya fasalin Nijeriya to a koma ta inda aka fara, kowane yanki ya koma matsayin sa kafin kirkirar gamammiyar Nijeriya.

 

LEAVE A COMMENT