Home gida SAUYA SHEKA: PDP Ba Za Ta Ba Atiku Takara Ba – Makarfi

SAUYA SHEKA: PDP Ba Za Ta Ba Atiku Takara Ba – Makarfi

342
0
SHARE

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ta ce ba za ta ba tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, tikitin tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben shekarar 2019 ba, sai ya bi dukkan matakan da aka shimfida.

Shugaban riko na jam’iyyar Sanata Ahmad Muhammad Makarfi, ya tabbatar da haka a wata ganawar sa da manema labarai.

A cewar sa, Atiku Bubakar, ne da kansa ya yanke shawarar komawa jam’iyyar PDP ba jam’iyyar ce ta yi zawarcin sa ba.

Ya kara da cewa sun yi maraba da kuma matukar murna da yadda Atikun ya dawo gida.

A halin da ake ciki dai  har yanzun Atiku, bai fito fili ya bayyana anniyar sa ta sake neman shugabancin kasa a babban zaben shekarar 2019 ba.

LEAVE A COMMENT