Home gida SAUYIN SHEKA: Atku Ya Roki Kwankwaso, Saraki, Tambuwal Su Dawo PDP

SAUYIN SHEKA: Atku Ya Roki Kwankwaso, Saraki, Tambuwal Su Dawo PDP

842
0
SHARE

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya roki wadanda su ka bar jam’iyyar PDP zuwa APC da su ka hada da Rabi’u Musa Kwankwaso, da Bukola Saraki, da Aminu Waziri Tambuwal su dawo jam’iyyar su ta asali.

Atiku Abubakar, ya ce babu sauran wata jam’iyyar siyasa a Nijeriya in ba jam’iyyar PDP ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya bayyana haka ne a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja.

Idan dai za a iya tunawa, a watan da ya gabata ne Atiku Abubakar ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.

LEAVE A COMMENT