Home gida SAYEN MAKAMAI: DAN NIJERIYA YA MAKA BA-AMURKE KOTU

SAYEN MAKAMAI: DAN NIJERIYA YA MAKA BA-AMURKE KOTU

425
0
SHARE

Wani dan Nijeriya Hima Abubakar da wani kasurgumin dillalin makamai da ke zama a kasar Amurka, sun gurfana a gaban kuliya a kan dala miliyan 246 na sayen makaman yaki da boko Haram.

Wata majiya ta ce tun a cikin shekara ta 2014 ne, aka amince da kwantaragin sayo makamai da jirage masu saukar ungulu da boma-bomai da alburusan da za a yaki ta’addanci a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Sai dai har tsawon shekara daya da bada kwangilar ba a kawo makaman ba, lamarin da ya sa Abubakar ya garzaya zuwa wata kotu da ke birnin California, inda ya gabatar da korafin cewa dillalin mai suna Dolarin bai ba su makamai da kimar su ta kai sama da dala miliyan 8 da rabi kamar yadda su ka yi yarjejeniya ba, lamarin da ya ce ya bata ma shi suna a idon hukumomin Nijeriya a matsayin sa na amintaccen mai sama wa sojoji makamai.

Sai dai wanda ake karar ya musanta dukkan bayanan da Abubakar ya gabatar, ya na mai shaida wa kotun cewa kudaden sayen makaman da ake zargin sa a kai ma na sata ne.

LEAVE A COMMENT