Home gida SHUGABANCI: OSINBAJO YA SANYA WA SABBIN DOKOKI 3 HANNU

SHUGABANCI: OSINBAJO YA SANYA WA SABBIN DOKOKI 3 HANNU

381
0
SHARE

Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya rattaba hannu a kan wasu dokoki uku da fadar shugaban kasa ta ce za su kawo gagarumin sauyi game da yadda ake gudanar da ayyukan gwamnati.

A cikin wata sanarwar da mai magana da yawun mukaddashin shugaban kasa Laolu Akande ya fitar, ya ce daya daga cikin sabbin dokokin, za ta sa ma’aikatun gwamnati su bada fifiko a kan hulda da kamfanoni da ‘yan kwangila na cikin gida a kan cinikayyar gwamnati.

An kuma sa hannu a kan dokar da za ta saukaka yanayin kasuwanci ga kamfanoni da ‘yan kasuwa masu zuba jari ko fitar da amfanin gona daga Nijeriya da kuma saukaka bangaren shige da fice.

Doka ta uku kuma ta na neman tilasta wa ma’aikatun gwamnati gaggauta mika bayanan kasafin shekaru uku ga ministan kudi da na kasafi da tsare-tsare a karshen watan Yuli.

Sanarwar ta ce kafin ya rattaba hannu a kan dokokin, Osinbajo ya gana da ministoci da shugabannin ma’akatun gwamnati da dokokin su ka shafa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

LEAVE A COMMENT