Home gida SIYASA: Malalisar Dokoki Ta Kasa Ta Sauya Tsarin Zaben Shekara Ta 2019

SIYASA: Malalisar Dokoki Ta Kasa Ta Sauya Tsarin Zaben Shekara Ta 2019

146
0
SHARE

Majalisar dokoki ta kasa ta amince da kudirin sauya dokar zaben shekara ta 2019.

 

Idan dai za a iya tunawa, hukumar zabe ta kasa ta fidda jadawalin zaben shekara ta 2019, sai dai kwamitin majalisar dokoki ya ce, za a fara gudanar da zaben ‘yan majalisun tarayya ne, sannan a yi na gwamnoni da na majalisun jihohi, yayin da  zaben shugaban kasa zan kasance na karshe.

 

Kwamitin ya ce, sabon tsarin zai ba kowane dan takara damar a zabe shi bisa ga cancantar sa ba tare da shiga inuwar wani ba.

 

Majalisar dokin dai, ta yi amfani da damar da kundin tsarin mulki na kasa ya tanadar a kan harkar zabe wajen sauya tsarin gudanar da zabe.

 

Shugaban kwamitin Sanata Suleiman Nazif na jam’iyyar APC, ya ce  sauyin bai yi wa kundin tsarin mulkin da ya ba hukumar zabe damar tsara jadawalin zabe karan tsaye ba.

LEAVE A COMMENT