Home gida TAKADDAMA: Na Shirya Kare Kai Na A Gaban Alkali – Afegbua

TAKADDAMA: Na Shirya Kare Kai Na A Gaban Alkali – Afegbua

159
0
SHARE

Mai Magana da yawun Janar Ibrahim Babangida Kasim Afegbua, ya wanke kan sa daga zargin fitar da sanarwar dole, bayan rundunar ‘yan sanda ta bayyana shi a matsayin wanda ta k enema ruwa a jallo.

 

Afegbua, ya ce a shirye ya ke domin kare kan sa a kotu, kuma zai mika kan sa ga hukumomi a ranar 7 ga watan Fabrairu.

 

Mista Afegbua dai, ya gabatar da jawabai a daren Lahadin da ta gabata, inda ya sanar da cewa Babangida ya soki lamirin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

 

Jim kadan bayan hukumar ‘yan sandan ta bayyana cewa ta na farautar sa, lauyoyin Afegbua sun wanke shi a kan lamarin.

LEAVE A COMMENT