Home HAUSA TALLAFIN MAI: Sanatoci Na Zargin Juna Da Hada Baki Da Kamfanin NNPC

TALLAFIN MAI: Sanatoci Na Zargin Juna Da Hada Baki Da Kamfanin NNPC

210
0
SHARE

Yan majalisar dattawa sun soki rahoton kwamitin harkokin man fetur na majalisar a kan rashin sanya al’amarin tallafin man fetur a cikin shi.

Sanatocin dai sun yi zargin cewa kamfanin NNPC ya yi saku-saku a cikin rahoton da kwamitin ya gabatar wa majalisa.

 Sun kuma soki shugaban kwamitin Sanata Kabir Marafa, a kan rashin sanya zancen tallafin mai da su ka yi zargin cewa fadar shugaban kasa ta biya ba tare da izini ko masaniyar majalisun dokoki ba.

Sanata Stella Oduah, ta ce ta na bada shawarar ayi watsi da rahoton, yayin da Sanata Godswill Akpabio ya ce rahoton zubar da mutuncin majalisar ne.

 A cikin rahoton, Sanata Marafa ya bada shawarwari 5 domin samun mafita daga rikicin man fetur.

 Bisa dukkan alamu dai, kwamitin ya na kokarin yin rufa-rufa a kan karin Naira 26 da gwamnati ke bada tallafi a kan kowace litar mai.

LEAVE A COMMENT