Home gida UMURNI: Buhari Ya Hana Ma’aikatu Da Hukumomi Daukar Sabbin Ma’aikata

UMURNI: Buhari Ya Hana Ma’aikatu Da Hukumomi Daukar Sabbin Ma’aikata

646
0
SHARE

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya soke damar daukar sabbin ma’aikata da dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati ke da ita har sai sun samu amincewar ofishin sa kai tsaye.

 

Buhari ya bayyana haka ne, yayin da ya ke gabatar da kasafin shekara ta 2018 a gaban majalisun dokoki na tarayya a Abuja.

 

A cewar sa, matakin zai saukaka wa gwamnati wajen kyautata amfani da kudade a kan ka’ida, wajen tafiyar da ayyuka da albashi ba tare da an rika samun gibi ba.

 

Ya ce hakan kuma, zai kara taimakawa, wajen bin ka’idojin da su ka kamata yayin daukar sabbin ma’aikata.

LEAVE A COMMENT