Home gida YAKI DA RASHAWA: Ibrahim Magu Ya Ziyarci Ofishin Hukumar JAMB

YAKI DA RASHAWA: Ibrahim Magu Ya Ziyarci Ofishin Hukumar JAMB

169
0
SHARE

Hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami’a JAMB, ta dage lokacin yin rajistar jarrabawar shekara ta 2018 zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu na shekara ta 2018.

 

Rajistaran hukumar Farfesa Is-haq Oloyede, ya ce kimanin mutane 1,451,691 ne su ka yi rigista, domin zana jarrabawar da su ka rufe yin rijistar.

 

Ya ce wadanda su ka yi rigistar a wannan shekarar kadan ne a kan wadanda su ka yi rijista a bara, wanda yawan su ya kai kimanin mutane miliyan daya da dubu dari bakwai, sannan kimanin mutane 39,663 su ka yi rijista domin shiga jami’a kai tsaye.

 

Oloyede ya bayyana haka ne, yayin da ya karbi bakuncin  shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu  a helkwatar hukumar da ke Abuja.

 

Farfesa Oloyede, ya ce hukumar za ta yi kokarin ganin sun yi aiki tare da hukumar EFCC domin yaki da cin hanci da rashawa.

LEAVE A COMMENT