Home HAUSA YAKI DA RASHAWA: Jami’an Tsaro Na Neman Izinin Binciken Neysom Wike

YAKI DA RASHAWA: Jami’an Tsaro Na Neman Izinin Binciken Neysom Wike

152
0
SHARE

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya da Hukumar EFCC da Jami’an tsaro na DSS sun shiga Kotu da Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike.

Jami’an tsaron dai, sun nemi Kotu ta basu dama su yi bincike a kan Nyesom Wike.

Gwamna Nyesom Wike dai ya kalubalanci wannan yunkuri na binciken sa a gaban Kotu,

Tun a shekarar da ta gabata ne, Gwamna Wike ya shiga Kotu da bukatar a haramta wa duk wasu Jami’an tsaro hurumin binciken gidan sa.

Sai dai Lauyan ‘Yan Sandan Nijeriya David Igbodo, ya nemi Kotun ta yi watsi da karar da Gwamnan ya kai a gaban ta.

LEAVE A COMMENT