Home gida YAKI DA TA’ADDANCI: Sojojin Kudu Sun Fi Na Arewa Bada Gudunmuwa –...

YAKI DA TA’ADDANCI: Sojojin Kudu Sun Fi Na Arewa Bada Gudunmuwa – Shettima

156
0
SHARE

Gwamnan Jihar Borno Kashin Shettima, ya ce Kwamandojin yaki da su ka fito daga sauran sassan Nijeriya sun fi takwarorin su na Arewa bada gudunmuwa da nuna bajinta wajen yaki da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram.

 

Shettima ya yi wannan furuci ne, a wajen wani taron sauraren ra’ayoyin jama’a da Gwamnatin Tarayya ta shirya a garin Maiduguri na Jihar Borno.

 

Gwamnan ya cigaba da cewa, galibin nasarorin da aka samu wajen yaki ta ta’addanci an same su ne a karkashin jagorancin kwamandojin da ba ‘yan Arewa ne ba.

 

Ya ce nasarorin da Rundunar Soji ta samu cikin makonni shida da su ka wuce a karkashin Janar Nicholas, ya dara nasarorin da aka samu a shekaru uku da su ka gabata.

 

Wadanda su ka halarci taron dai sun hada da Ministan Tsaro Mansur Dan-Ali, da Ministan Harkokin Cikin Gida Abdulrahman Dambazau da kuma Ministan yada Labarai da Al’adu Lai Mohammed.

LEAVE A COMMENT