Home gida ZABE: INEC ta Cire Sunayen ‘Yan Kasashen Waje 190 da Aakayiwa Rajista

ZABE: INEC ta Cire Sunayen ‘Yan Kasashen Waje 190 da Aakayiwa Rajista

280
0
SHARE

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta cire sunayen mutane 190 wadanda ba ‘yan Najeriya ba kuma suka mallaki katin zabe na din-din din.

Sanarwan hakan ta fito ne daga bakin daraktan wayar da kan jama’a kan harkar katin zabe Oluwole Osaze-Uzzi, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce idan ba a manta ba hukumar kula da masu shige da fice, ta ce ta karbi wasu katunan zaben Najeriya da katin shedar zama dan kasa daga wasu baki wadanda suka ce anyi musu ragista.

Osaze-Uzzi ya tabbatar da cewa suna yin dukkan mai yiwuwa wajen ganin an tsaftace aikin yin rajistan dan gudun yiwa wadanda ba ‘yan kasa ba.

LEAVE A COMMENT