Home gida ZABEN 2019: Arewa Ce Za Ta Fitar Da Shugaban Kasa a PDP...

ZABEN 2019: Arewa Ce Za Ta Fitar Da Shugaban Kasa a PDP – Orji Kalu

341
0
SHARE

Tsohon Gwaman Jihar Abia Orji Uzor Kalu, ya ce dole a bar yankin Arewa ya karasa sauran shekarun sa 4 na shekaru 8 a kujerar Shugabancin Kasa, sauran yankuna kuma su hakura har sai shekara ta 2023.

 

Orji Kalu ya bayyana wa manema labarai haka ne, jim kadan bayan kammala wata ganawar sirri da ya yi da tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida a gidan da ke Minna a jihar Neja.

 

Ya ce lallai dan Arewa ne zai fito takarar Shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP ko da kuwa Buhari ba zai kara tsayawa takara ba.

 

A cewar sa, duk da shi ma ya na da ikon fitowa takara, amma ya na kan fahimtar wannan lokaci ne na Arewa, ya na mai cewa adalci ya na da matukar muhimmanci, don haka dole Arewa ta karasa shekarun ta.

 

LEAVE A COMMENT