Home gida ZABEN 2019: Ba Mu Tsaida Dan Takara Ba – Dattawan Arewa

ZABEN 2019: Ba Mu Tsaida Dan Takara Ba – Dattawan Arewa

246
0
SHARE

Kungiyar Dattawan Arewa ta musanta rahotannin da kafofin yada labarai su ka yada cewa sun bada shawarar sake tsayar da shugaba Buhari a matsayin dan takara karo na biyu.

A wata hira da ya yi da manema labarai, an ambato shugaban kungiyar Paul Unongo ya na cewa, yankin Arewa ya tsayar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takara a zaben shekara ta 2019.

Sai dai daya daga cikin jiga-jigan kungiyar Captain Bashir Sodangi, ya ce duk abin da Unongo ya fada ra’ayin kan shi ne ban a kungiya ba.

 Ya ce kungiyar ba ta taba tattaunawa game da siyasar shekara ta 2019 ba balle ta tsayar da dan takara.

LEAVE A COMMENT