Home gida ZABEN 2019: Ba Mu Yarda Fayose Ya Yi Takarar Shugaban Kasa Ba...

ZABEN 2019: Ba Mu Yarda Fayose Ya Yi Takarar Shugaban Kasa Ba – Makarfi

527
0
SHARE

Shugaban jam’iyyar PDP Sanata Ahmed Makarfi, ya jaddada cewa dan arewa ne zai yi takarar shugabancin Nijeriya a zaben shekara ta 2019 a karkashin jam’iyyar PDP.

 

Makarfi ya bayyana haka ne, a lokacin da ya ke bayani a wajen taron da jiga-jigan jam’iyyar PDP na arewacin Nijeriya a ranar Talatar da ta gabata.

 

Jam’iyyar PDP dai ta cimma matsaya a kan cewa, yankin kudancin Nijeriya ne zai shugabanci jam’iyyar, yayin da yankin arewa zai yi takarar shugabancin kasa a shekara ta 2019.

 

Sanata Makarfi, ya kuma jaddada muhimmancin hadin kai da mutunta juna da kuma manufofi da tsare-tsaren jam’iyyar domin samun nasara a zabubbukan da ke tafe.

 

LEAVE A COMMENT