Home gida ZABEN 2019: INEC Ta Ce Zata Yada  Sakamakon Zabe Ta Hanyar Tauraron...

ZABEN 2019: INEC Ta Ce Zata Yada  Sakamakon Zabe Ta Hanyar Tauraron Dan Aadam

295
0
SHARE

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa  INEC ta ce zata yada sakamakon zaben 2019 da za a gudanar ta hanyar sadarwa da ke amfani da na’uran tauraron dan Adam.

INEC ta na neman taimakon hukumar kula da tauraron dan adam ta kasa NIGCOMSAT saboda amfani da tauraron ta wajen yada sakamakon zaben kowacce mazaba a fadin Nijeriya.

Shugaban hukumar Ferfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci hedkwatar kukumar kula da tauraron dan’adam ta kasa da ke Abuja.

Babbar daracktar hukumar NIGCOMSAT Abimbola Alale, ta ce hukuma ta  a shirye ta ke da ta ba INEC goyon baya wajen yada sakamakon zabe.

A shekarar 2019 ne dai INEC za ta gudanar da zabuka a karon farko a karkashin jagorancin Farfesa Mahmood Yakubu idan wannan kudiri ya kai ga samun nasara.

Idan dai za a iya tuna wa, a watannin baya hukumar INEC ta fitar da jadawalin zaben 2019 wanda za a gudanar a watan febarerun shekarar.

LEAVE A COMMENT