Home gida ZARGI: Za Mu Cigaba Da Binciken Ibrahim Idris – Majalisar Dattawa

ZARGI: Za Mu Cigaba Da Binciken Ibrahim Idris – Majalisar Dattawa

289
0
SHARE

Majalisar dattawa, ta jadadda kudurin ta na ci-gaba da gudanar da bincike a kan zargin da Sanata Isah Misau ya yi wa shugaban ‘yan sandan Nijeriya Ibrahim Idris.

 

Shugaban kwamitin da’a na majalisar dattawa Sam Anyanwu, ya ce kwamitin zai cigaba da binciken tun da ba a shigar da shi cikin takardar da ministan shari’a da babban mai shari’a na tarayya su ka gabatar a kan Misau a madadin Ibrahim Idris.

 

A ranar 4 ga watan Oktoba na shekara ta 2017, majalisar ta yanke shawarar binciken Idris a kan zargin da Misau ya yi masa game da cin hanci da rashawa.

 

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, ya umarci kwamitin da’a na majalisar ya binciki abubuwan da su ka sa Misau ya yi ritaya daga hukumar ‘yan sanda ta Nijeriya.

 

Saraki ya kuma kafa wani kwamitin musamman, domin bincike akan zargin da ake yi wa hukumar ‘yan sanda ta Nijeriya da Ibrahim Idris game da naira biliyan 120 na ayyuka tsaro da ake karba a kowace shekara daga manyan mutane da kamfanoni masu zaman kan su Nijeriya.

LEAVE A COMMENT