Home gida ZARGIN RASHAWA: Ina Jiran Sammacin Kotu – Danladi Umar

ZARGIN RASHAWA: Ina Jiran Sammacin Kotu – Danladi Umar

274
0
SHARE

Shugaban kotun ladaftar da ma’aikata mai shari’a Danladi Umar, ya ce a shirye ya ke ya kare kan sa a kan zargin rashawa da hukumar EFCC ta yi masa.

 

Hukumar EFCC ta na tuhumar Danladi Umar ne bisa zargin ya karbi cin hancin Naira miliyan 10 daga hannun wani tsohon jami’in hukumar Kwastam.

 

Sai dai Danlladi Umar, ya ce kawai ana yi ma shi bi-ta-da-kulli ne da kuma kotun sa, don haka y ace su na jiran sammacin kotu, daga baya su san yada abubuwa za su wakana.

 

Dalladi Umar, ya tuhumi hukumar EFCC da rashin tsayawa a kan magana daya, ya na mai cewa laifin da su ke tuhumar sa a kai sau biyu kenan su na wanke shi a kan sa.

 

Idan dai za a iya tunawa, EFCC ta shigar da karar Danladi Umar ne a ranar 25 ga watan Junairu, amma babu alkalin da aka nada ya saurari shari’ar.

LEAVE A COMMENT