Home HAUSA DAMBARWA: DSS Ta Gayyaci Mai Magana Da Yawun Ttsohon Shugaban Kasa Babangida

DAMBARWA: DSS Ta Gayyaci Mai Magana Da Yawun Ttsohon Shugaban Kasa Babangida

349
0
SHARE

Hukumar tsaron DSS  ta gayyaci mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida, Kassim Afegbua.

Mr Kassim ya samu  gayyatar ce, ta wayar salula inda hukumar ta bukaci ya halarci a ofishin ta kafin karfe 11 na safiya alhamis dinnan tare da lauyan sa Kayode Ajulo.

Rahotanni sun ce, hukumar DSS ta gayyace shine  bayan ya mika kansa ga hukumar ‘yan sanda a shelkwatan ta da ke Abuja, sakamakon rubutun daya yi wanda zai iya tayar da hankalin jama’a a madadin tsohon shugaban kasa, Ibrahim badamasi Babangida.

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne akai ta yamadidi akan batun cewa, tsohon shugaba Babangida ya bukaci shugaba Buhari kada ya sake takara a 2019 batun ha ya fito fili ya karya ta.

Leave A Comment