Home HAUSA Dubu Ta Cika: An Gabatar Da Matar Da Ta Damfari Mutane A...

Dubu Ta Cika: An Gabatar Da Matar Da Ta Damfari Mutane A Fadar Shugaban Kasa

72
0
SHARE

Hukumar tsaro farin kaya DSS, ta gabatar da wata mata mai suna Amina Mohammmed a gaban ‘yan jarida, bisa zargin ta da amfani da fadar shugaban kasa ta na damfarar mutane.

A cewar hukumar DSS, matar ta na shiga cikin fadar shugaban kasa ba tare da izini ba.

ta ce matar ta rika yi wa wasu manyan jami’an gwamnati sojin-gona, ciki kuwa har da matar gwamnan jihar Kogi.

Kakakin hukumar tsaro ta DSS Peter Afunaya, ya ce matar ta rika shiga cikin gidan matar shugaban kasa A’isha Buhari, kuma

ta na amfani da sunaye daban-daban domin shiga cikin fadar shugaban kasa.

Peter Afunaya ya cigaba da cewa, ana zargin matar da damfarar wani dan kasuwa naira miliyan 150 a shekara ta 2017, kuma ta rika amfani da sunan A’isha Buhari wajen damfarar mutane masu neman kwangila a fadar shugaban kasa.

Lamarin dai ya na zuwa ne, watanni uku bayan A’isha Buhari ta zargi wani jami’in da ke kula da tsaron lafiyar ta da amfani da sunan ta wajen karbar kudade daga wajen mutanen da ke neman alfarma a fadar shugaban kasa.

Leave A Comment